ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto ministan ahrkokin cikin gida na kasar Fred Matiangi yana fadar haka a jiya Laraba ya kuma kara da cewa sansanonin da za’a rufen sun hada da ta Dadaab da kuma Kakuma wadanda ‘yan gudun hijiran Somalia suke samun mafaka a cikinsu tun kimani shekaru 30 da suka gabata.
Labarin ya kara da cewa a shekara ta 2016 ma gwamnatin kasar ta Kenya ta kuduri anniyar rufe sansanonin yan gudun hijirar amma hukuncin wata kotu a kasar ta hanata yin hakan.
Fred Matiangi ya fadawa reuters cewa ta bawa hukuma mai kula da ‘yan gudun hijira ta MDA UNHCR kan ta tsara batun rufe sansanonin guda biyu wadanda suke da mutane kimai nan da kwanaki 14. Sansanonin guda biyu dai suna dauke da mutane kimani 190,000.
Daga karshe ministan ya kammala da cewa basu dau wannan matakin don matsalolin diblomasiyya da suka sa gwamnatin kasar Somalia ta kira jakadanta zuwa gida ba ko kuma batun kan iyakokin kasashen biyu ta ruwa.